Senegal ta kama bakin hauren Afirka da ke neman shiga Turai
March 18, 2025Gwamnatin Senegal ta sanar da kama bakin haure 59 da ke neman shiga Turai ba bisa ka'ida ba, a wani kauye da ke kusa da gabar tekun Atlantika, wanda ya kawo adadin mutanen da aka kama zuwa 400 a cikin kwanaki hudu. Cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Facebook, rundunar Jandarmar Senegal ta ce wadannan bakin hauren sun fito ne daga yankin yammacin Afirka baki daya, musamman daga kasar Guinea da Gambiya, da Côte d' Ivoire da kuma Saliyo.
Karin bayani: MSC: kalubalen kwararar bakin haure a duniya
Yawancin bakin hauren, wadanda galibinsu matasa marasa aikin yi ne, na neman inganta rayuwarusu ta hanyar bin hanyar teku mai hadari don isa Turai ta barauniyar hanya. A shekarar 2024 da ta gabata, kusan mutane 47,000 ne suka yi yunkurin shiga Turai ta teku daga yammacin Afirka, a cewar hukumar Frontex. Wannan adadin ya karu da kashi 18% idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata.Fiye da bakin haure 10,400 ne suka mutu ko kuma suka bace a teku a lokacin da suke kokarin isa Spain a shekarar 2024, a cewar wata kungiya mai zaman kanta Caminando Fronteras.