Senegal ta haramta amfani da babura a kan iyakokinta da Mali
July 26, 2025Hukumomin Senegal sun kafa dokar hana amfani da babura da dare a wani yanki na gabashin kasar, bayan da ‘yanbindiga suka yi amfani da babura wajen kai hare-hare a wasu garuruwa da ke kan iyakarta da kasar Mali.
Umarnin na wannan makon ya bayyana cewa an kafa wannan haramci ne "saboda dalilan tsaro,” bayan da ‘yanta'adda suka kai hari kan sansanonin sojoji a wasu garuruwan Mali a ranar 1 ga watan Yuli, inda aka kashe a kalla mutum guda.
Senegal: Jama'a sun fara komawa gida bayan lafawar lamura
Daya daga cikin garuruwan Mali da aka kai wa hari, wato Diboli, na da tazarar da ba ta kai mita 500 ba daga garin Kidira da ke Senegal.
Senegal da Benin za su samar da sabon numfashi ga UEMOA
Dokar hana babura daga tsakar dare zuwa asuba din ta shafi yankin Bakel da ke Senegal, wanda ke kusan kilomita 230 a kan iyaka da Mali.