Casamance: Tabbatar zaman lafiya ya sa Jama'a komawa gida
July 2, 2025Mutanen da suka tsere daga yankin saboda tashe-tashen hankula na kungiyar 'yan aware ta Casamance a yanzu sun fara komawa gida a karkashin wani shirin da shugaban Senegal Bassirou Diomaye Faye ya kaddamar.
Tun daga farkon shekarun 1980 zuwa 2005, bayan tsagaita bude wuta, a yankin Casamance an yi ta shan artabu tsakanin dakarun 'yan tawaye na Movement of Democratic Forces of Casamance (MFDC), karkashin jagorancin Abbe Diamacoune Senghor, da dakarun gwamnatin Senegal, lamarin da ya yi sanadin mutuwar dubban daruruwan rayukan jama'a yayin da wasu dubbai suka bar yankin.
Tun bayan samun ‘yancin kai na Senegal a shekarar 1960, al'ummar Casamance sun yi mafarkin samun ‘yancin cin gashin kansu, kuma tsohon shugaban kasar Léopold Sédar Senghor ya kyankasa musu wannan albishir to amma daga baya abin ya gagara aka shiga yaki.
Mazauna wannan yanki,na Casamance wadanmda galibinsu Dioula ne daman sun riga sun yi tawaye ga yunkurin mulkin mallaka na Faransa da kuma aikin bauta. A yanzu da sannu a hankali da yawa da suka fice daga yankin bayan goman shekaru sun fara komwa gida Casamance. Dominique Dasylva ya koma kauyensu da ke cikin yankin na Casamance bayan kusan shekaru 35 na hijira.
A Shekara ta 1986, dole ne na fice daga Casamance. Sannan kuma a cikin 1992, an tilasta mini yin gudun hijira. Na kasance a Dakar, amma Dakar ban ji dadin rayuwar ba, yanzu da komai ya daidata an samu kwanciyar hankali na dawo gida Casamance mun manta da abinda ya wuce.
Sama da shekaru 40 da ‘yan tawayen na Casamance suka yi suna yin yaki da gwamnatin Dakar domin neman 'yancin gashin kai Juliette Mendy iyayenta sun haifeta a lokacin suna yin gudun hijira a yanzu ta koma garin kakanninta a Casamance
"An haife ni a Dakar, mahaifina kullum yana magana da ni akai-akai a kan Casamance cewa nan ne asilinsu yau na zo na ga cibiyar iyaye ne da kakkanina na ji dadi wannan abin alfahari ne a gare ni".
Sama da kauyuka 300 na Casamance aka share daga taswirar Senegal sakamakon yakin da aka yi fama da shi. Dubun dubatar mutanen da suka tsere daga rikicin sun fake a manyan biranen kasar irinsu Ziguinchor da Dakar babban birnin kasar, yayin da wasu suka zabi tafiya kasashe makwabtaka irin su Guinea-Bissau da Gambia. Nouha Cissé, masasnin tarihi a jamiar Ziguinchor ya ce a yanzu sai an sake raya yanki.
Komawarsu abu ne mai matuƙar muhimmanci wajen farfado da tattalin arzikin yankuna dabam-dabam waɗanda rikicin ya shafa. Da sake dawo da ayyuka da al'adu kamar yadda suka bunkasa kafin a sami wannan bala'in na yaki. Shugaba Bassirou Diomaye Faye da firaminista Ousman Sonko wadanda su dukkanisu yan yankin Casamance sun ba gudun muwa sossai wajen ganin an kawo karshen yankin na Casamance kwata-kwata.