Sauyin 'yan wasa mafi tasiri a gasar Bundesliga
Tafiyar Florian Wirtz daga Bundesliga, ta janyo rasa 'yan wasa masu tasiri. Wadanne 'yan wasa ne suka fita daga gasar, sannan wadanne ne suka sauya sheka a gasar ta Bundesliga kana wadanne ne suka shiga?
Florian Wirtz daga Bayer Leverkusen zuwa FC Liverpool
A cikin yanayin tarihi, guda cikin kwararrun 'yan wasan Jamus ya sauya sheka kan kudi Euro miliyan 150. Maimakon ya koma FC Bayern da kila za ta so ta saye shi, saboda kwarewarsa wajen iya sarrafa kwallo. Saidai Wirtz ya zabi ya koma kungiyar FC Liverpool ta Ingila. An dai saye shi a kan kudi Euro miliyan 125, inda za a rinka biyansa albashin Euro miliyan 12 zuwa 15 a shekara.
Jeremie Frimpong daga Bayer Leverkusen zuwa FC Liverpool
Shi ma Jeremie Frimpong abokin wasan Wirtz a kungiyar Leverkusen ya bi sahu, inda dan kasar Netherlands din ya koma Kungiyar Liverpool a kan kudi kimanin Euro milyan 35. Za dai a iya cewa, Frimpong ya koma gida. Ya girma a Ingila tun yana da shekaru bakwai a duniya, inda ya fara samun horo a kungiyar Manchester City ta 'yan kasa da shekaru 19.
Hugo Ekitiké daga Eintracht Frankfurt zuwa FC Liverpool
"Hugo ya samu ci-gaba cikin shekara daya da rabi da ya yi tare da mu", a cewar Markus Krösche darakta a kunguyar Frankfurt. Ita dai Eintracht Frankfurt, ta samu kudin sauyin sheka da ya kai Euro milyan 95 daga kungiyar Liverpool ta Ingila. Hugo Ekitiké dan kasar Faransa mai shekaru 23 da haihuwa ya jefa kwallaye 15 a wasannin Bundesliga, ya kuma taimaka an zura kwallaye takwas a raga.
Jonathan Burkardt daga Mainz zuwa Eintracht Frankfurt
Bayan shekaru 10 a kungiyar Mainz, a karshe dan wasan Jamus Jonathan Burkardt ya koma kungiyar abokan hamayya. Dan wasan mai shekaru 24 da haihuwa ya tsallaka zuwa wasan neman cin kofin zakarun Turai tare da Mainz, amma yanzu zai yi wasan tare da kungiyar Eintracht Frankfurt. Burkardt da ya sanya hannu kan kwantiragi har zuwa shekara ta 2030, an saye shi kan kudi Euro milyan 23 har da kudin gata.
Noah Darvich daga Barcelona zuwa Stuttgart
Mai shekaru 18 da haihuwar, na cikin 'yan wasan Jamus matasa masu tasiri. Ya soma da wasan cin kofin Turai da na duniya na 'yan kasa da shekaru 17 da haihuwa, a shekara ta 2023. Ya koma taka leda a tawagar matasa ta kungiyar Barcelona, shekaru biyun da suka gabata. Tsohon dan wasan matasan kungiyar Freiburg, ya saka hannu kan kwantiragi da kungiyar Stuttgart har zuwa shekara ta 2029.
Jobe Bellingham daga AFC Sunderland zuwa Borussia Dortmund
Jobe Bellingham ya sake koma wa kungiyar Borussia Dortmund da yake da dangantaka da ita, inda ya bi sawun yayansa Jude Bellingham a kungiyar. Mai shekaru 19 da haihuwa ya baro kungiyar AFC Sunderland ta Ingila, a kan kudi kimanin Euro milyan 30 zuwa kungiyar Dortmund. Ya saka hannu kan kwantiragi da Borussia Dortmund, har zuwa shekara ta 2030.
Jonathan Tah daga Bayer Leverkusen, zuwa Bayern Munich
Ya so ya koma kungiyar Bayern Munich tun lokacin bazarar shekarar da ta gabata, amma an samu akasi wajen kammala yarjejeniyar. Dan wasan bayan ya sauya sheka, bayan kwantiraginsa da kungiyar Leverkusen ta kawo karshe. Kungiyar Bayern Munich, ta jima tana tsarin dauko Tah. A yanzu akwai kudin sauyin sheka daga Euro milyan biyu zuwa hudu, ya danganta da nasarar da ya samu.
Jarell Quansah daga FC Liverpool zuwa Bayer Leverkusen
Bayer Leverkusen ta maye gurbin Jonathan Tah da dan wasan kungiyar Liverpool ta Ingila 'yan kasa da shekaru 21 a wasannin cin kofin Turai, inda aka kashe kudi kimanin Euro milyan 30 kan kwantiraginn Jarell Quansah har zuwa shekara ta 2030. Kudin zai iya kai wa Euro milyan 40, idan aka hada da kudin garabasa. Mai shekaru 22 a duniyar, ya kafa tahiri a kan wannan kudin a kungiyar ta Leverkusen.
Leroy Sané daga Bayern Munich zuwa Galatasaray
Bayan shekaru biyar a kungiyar Bayern Munich ta Jamus, ba ya bukatar sake saka hannu da kungiyar Bayern Munich. Maimakon haka Leroy Sané ya zabi komawa zuwa Galatasaray da ke kasar Turkiyya a matsayin sabon babi, ta yi wu saboda karin kudi da zai samu. Sané zai karbi kimanin Euro milyan 12 lokacin kakar wasanni, karkashin sabuwar kwantiraginsa.
Mark Flekken daga FC Brentford zuwa Bayer Leverkusen
Dan kasar Netherlands mai tsaron raga Mark Flekken ya koma kungiyar Bayer Leverkusen daga wasanin Premier ta Ingila, inda ake sa ran zai maye gurbin Lukas Hradecky a matsayin mai tsaron raga. Ya kasance mai tsaron raga na kungiyar Freiburg daga shekara ta 2021 zuwa ta 2023.