Sauya sheka: Farin jinin APC ko neman biyan bukata?
April 24, 2025A yayin da ake kara kusantar manyan zabuka a Najeriya, sannu a hankali jam’iyyar APC mai mulki na ci gaba da hadiye 'ya'yan adawa a wani abun da ke aike sako bisa makomar dimukuraddiyar kasar. Kama daga PDP ya zuwa Labour Party da NNPP ta masu kayan dadi , masu adawar Najeriyar na asarar jiga-jigan 'y'ayansu da ke ta karkata zuwa jam’iyyar APC mai mulki. Akalla 'yan majalisar dattawa 10 ne suka yi sauyin sheka ya zuwa APC, baya ga gwamnan Delta da kila ma wasu gwamnoni guda biyu daga yankin Niger-Delta, a wani abun da ke nuna alamun karkatar fagen siyasar Najeriyar zuwa kasa mai jam’iyya guda daya.
Karin bayani: Manyan jam'iyyun Najeriya na rasa 'ya'yansu
Sauyin shekar ya fara jawo damuwa tsakanin shugabannin jam’iyyun da ke tunanin hadaka, amma kuma ke Kallon kwashe 'ya'yansu zuwa APC ta masu tsintsiya, ciki har da Aminu Abdusallam, da ke zaman mataimakin gwamnan kano, jihar da ta yi asarar daya daga cikin dattawanta a majalisar dattawa ta kasar.
Ana Kallon sauyin shekar a matsayin barazana a batun hadaka da masu adawar ke yi wa kallon cewar za ta iya sauya fagen siyasar kasar. Ita kanta jam'iyyar PDP da ke da fatan jagorantar hadakar na fuskantar barazanar rasa 'ya'yanta. Akalla gwamnoni guda uku na kudancin tarayyar Najeriyar daga jam’iyyar PDP ne ake ji suna shirin sauyin shekar. Sai dai 'yan lemar PDP suka ce suna shirin dorawa ko ana ha maza ha mata, a fadar Ibrahim Abdullahi, da ke zaman kakakin jam’iyyar na kasa.
Karin bayani: Mece ce makomar jam'iyyun adawa a Najeriya?
Tsoro da neman bukatar kai ne ke kai mafi yawan masu siyasar sauyin shekar zuwa jam'iyyar da ke mulkin Najeriya. Ko da Farfesa kamilu Sani Fage, da ke zaman kwarrare ga siyasar tarayyar Najeriyar, sai da ya ce sauyin shekar na yin illa ga kokarin samun zabi da kila neman sauyi a siyasar tarayyar Najeriyar.
Karin bayani: Sabani ya kunno kai tsakanin jiga-jigan SDP da PDP
Sauyin shekar na zaman salo na masu tsintsiya PDP a shekarun mulkinta, kafin ta yi cikar kwari ta kai ga fashewa sakamakon rigingimun cikin gida tsakanin 'ya'yanta.