Alamu na nuna za'a samu jinkiri wajen bayyana sakamakon zaben shugaban kasa dana 'yan majalisu a Ghana, bayan da hukumar zaben kasar, ta ce za ta sake nazarin alkaluman kidddiga, dangane da fargabar yiwuwar magudi.
Hukumar zaben Ghana ta yi kiran kwantar da hankula yayin da ake jiran sakamako, tana mai cewa za ta bi diddigin dukkan sakamakon da aka kawo daga mazabu.Fafatawa a zaben dai tafi zafi ne tsakanin Shugaba John Mahama da kuma babban abokin hamaiyarsa Nana Akufo Ado.