A cikin shirin za a ji cewa a Jamhuriyar Nijar a wannan litinin ce ake bukukuwan zagayowar ranar hadin kasa da ake kira journee de la Concorde. An kaddamar da ranar ce dai tun tunawa da yarjejeniyar sulhu da ajiye makammai tsakanin gwamnati da 'yan tawayen a wancen lokaci.