Saudiyya ta dauki matakan kare lafiyar maniyyata
June 4, 2025Da yanayin zafi sama da digiri 40 na ma'aunin celcius, a yau ne mahajjatan sanye da Ihrami suka isa garin Mina da ke bayan Makkah, inda za su yi zama na tsawon kwanaki aikin hajjin, wanda zai fara da zuwa Dutsen Arafa a gobe Alhamis. Wurin da fiyayyen halitta Annabi Muhammad (Tsira da amincin Allah su kara tabbata a gareshi) ya yi hudubarsa ta karshe.
Hukumomin Saudiyya sun ce kimanin mahajjata miliyan 1.5 ne suka isa kasar domin gudanar da aikin hajjin bana, daya daga cikin rukunnan addinin Musulunci guda biyar da tilas ne dukkan musulmi ya gudanar sau daya a rayuwa, idan yana da sukuni.
Domin gujewa maimaita abun da ya faru ba, lokacin da mutane 1,301 suka mutu saboda yanayin zafi da ya kai sama da digiri 51, hukumomi sun bullo da wasu sabbin matakai da ka'idoji da ya zama wajibi maniyyatan su martaba.