Saudiyya ta aiwatar da hukuncin kisa kan mutum takwas
August 3, 2025Kamfanin dillancin labaran Saudiyya na SPA, ya ruwaito cewa an aikwatar da hukuncin kisa ne kan wasu 'yan asalin Somaliya hudu da kuma 'yan Habasha uku a kudancin yankin Najra, bisa laifin shigar da wani nau'in wiwi cikin masarautar Saudiyya. Yayin da hukunci ya hau kan dan Saudiya guda bisa laifin kashe mahaifiyarsa.
Karin bayani: Wasu kasashen duniya sun soke hukuncin kisa
Tun farkon wannan shekarar ta 2025, Saudiyya ta zartar da hukuncin kisa kan mutane 230. Masana na alakanta hakan ne da shirin da kasar ta kaddamar a shekarar 2023 na yaki da safarar kwayoyi. Masu fafutukar kare hakkin dan Adam na cewa, masarautar na ci gaba da zubar da kimarta da ke nuna sauki cikin al'amuranta, wanda shi ne ginshikin shirin yarima mai jiran gado, Muhammad bin Salman na kawo sauyi.