Sarkin musulmin Najeriya ya yi Allah wadai da hare haren Abuja
August 31, 2011Sarkin musulmi na Tarrayr Najeriya ya yi allah wadai da hare haren ƙunar bakin waken da aka kai a makon jiya a cibiyar Majalisar Ɗikin Duniya dake a birnin Abuja wanda a cikin sa mutane 23 suka cikka wanda, kuma ake ɗora alhakin sa akan ƙungiyar nan da aka fi sanni da sunnan boko haram.
Sultan Muhammad sa'ad Abubakar na Sokoto da ke yin jawabi ga musulmi a ƙarshen watan ramdan; ya yi kira ga yan ƙungiyar da su shiga tattaunawa da gwamnatin a maimmakon kai hare hare ta'adanci.wannan shi ne karo na biyu kennan a cikin sa'a guda da da sarkin ke yin tsokacin akan tashin hankali da ake fama da shi na yan ƙungiyar boko haram. Kuma hukumomin tsaro na Tarrayar Najeriyar' sun ce sun kama wasu mutane guda biyu dangane da bincikken da ake gudanarwa akan hare haren. Sannan suka ce sun gano wanda ya tsara harin wanda ake kira da sunnan Mahaman Nur wanda bai daɗe ba da dawo ba daga ƙasar Somaliya.
Mawallafi: Abdourahamane Hassane
Edita : Usman Shehu Uman