Sarkin Jordan ya bukaci tsagaita wuta a Gaza
February 13, 2024Da suke magana a fadar White House shugabannin biyu sun yi gargadi kan duk wani harin kan mai uwa da wabi a kutsen da Israila ta ke son yi ta kasa a birnin Rafah da ke kudancin Gaza inda mutane fiye da miliyan daya suke mafaka.
Karin Bayani: MDD ta bukaci da a dakatar da Isra'ila daga kai hari a Rafah
Sar Abdallah ya ce abin takaici, daya daga cikin yake yake mafi muni a wannan zamani na cigaba da aukuwa a Gaza, an kashe mutane kusan 100,000 wasu sun jikkata wasu sun bata yawancinsu mata da kananan yara. Ba za mu zuba ido wannan al'amari ya ci gaba ba. Muna bukatar tsagaita wuta mai dorewa a yanzu
Amurka dai ta fusata aminanta na Gabas Ta Tsakiya inda ta ki yin kiran cikakkiyar tsagita wuta inda ta ke cewa ta na goyon bayan yunkurin Israila na murkushe Hamas.