Sarki Charles na Burtaniya ya karrama mamatan hadarin Indiya
June 14, 2025Sarki Charles na Burtaniya bisa rakiyar iyalan masarautar, sun karrama daruruwan mutanen da suka mutu a hadarin jirgin saman kasar Indiya, yayin faretin ban-girma na taya shi murnar zagayowar ranar haihuwarsa a wannan Asabar.
Fadar Buckingham ta ce dukkan iyalan gidan sarautar sanye da kakin soja, sun yi shiru na minti daya, hanayensu daure da bakin kyalle na nuna alhini a birnin London.
Sarki Charles na uku shi ne kuma jagoran kungiyar kasashen rainon Ingila ta Commonwealth, kuma Indiya da Canada mambobi a kungiyar.
Karin bayani:Mutum daya ya tsira a hatsarin jirgin saman Indiya
Ko a shekarar 2017 mahaifiyarsa Sarauniya Elizabeth ta biyu ta gudanar da makamaciyar karramawar, don nuna alihinin mutuwar mutane 72 sanadiyyar gobara a dogon ginin nan na Grenfell da ke London.