Sanyin hunturu ya janyo salwantar rayuka a Turai
February 2, 2012Adadin wadanda suka rasu sakamakon sanyi a nan Turai ya daga zuwa fiye da 120, ga wadanda ke zama a gabashin Europe yanayin ya kai intaha. A kasar Ukraine sanyi na reto tsakanin maki 30 zuwa 63 kasa da sifili bisa ma'aunin sanyi da zafi kamar yadda hukumar kula da fararen hukar kasar ta bayyana. Yaawancin irin wadanda suka rasu irin marasa galihun nan ne da basu da matsugunen kirki. Haka nan ma sauran kasashen suna kokarin su yi kokawa da dusar kankara. A kasar Turkiyya dusar kankarar ta hana sufuri ta kuma shafi wutar lantarki. Labarin bai sauya ba a arewacin Italiya, inda can ma dusar kankarar ta tare hanyoyin mota da na jiragen kasa. Kimanin mutane 50 suka rasu sakamakon hadarurrukan da ke da nasaba da dusar kankarar, mafi yawancinsu kuma tsofaffi.
Mawallafiya: Pinado Abdu-Waba
Edita: Umaru Aliyu