Samar da tsaro a Katsina ya gagari kundila
August 20, 2025Adadin wadanda suka mutu sakamakon harin 'yan bindiga akan masu sallar asuba a garin Malumfashi na jihar Katsina ya dada karuwa. Majiya ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewar hari da 'yan bindigar suka kai kan masallatan a unguwar Mantau ya kai fiye da 30 a wannan Laraba.
Harin 'yan bindiga ya halaka mutane a Katsina da ke Najeriya
Tun daga farko dai mahukunta a Katsina sun sanar da mutuwar mutane 13 ne jim kadan bayan harin 'yan bindigar, duk da yarjejeniyar sulhu da hukumomin suka rattaba hannu da wasu dauke da makamai da barayin daji.
Katsina dake yankin arewa maso yammacin Najeriya na guda daga cikin jihohin yankin da ke fama da matsalolin tsaro, kama daga barayin daji masu garkuwa da mutane don neman kudin fansa da 'yan t'adda.
Katsina: Yaushe za a magance matsalar tsaro?
A baya bayan nan gwamnatin jihar ta nemi daukin shugaban kasa da gwamnatin tarayya, da nufin magance matsalolin tsaron yankin da ke neman ya gagari kundila