Samar da mafita ga matsalar kudin nahiyar Turai
November 19, 2011Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta gana da fraministan Burtaniya David Cameron a birnin Berlin na nan Jamus ,domin tattaunawa dangane da yadda zasu haɗa karfe da ƙarfi domin shawo kan matsalar kuɗi da ƙasashen ƙungiyar Tarayar Turai ke fuskanta.Da take yin jawabi a wajan saduwar Merkel ta ce gurin kasashen biyu shi ne na ganin sun cimma gyara al'amuran kuɗaɗen su.
Ta yadda zasu tabbatar da cewa ƙarin kasafin kuɗinsu bai zarta addadin da ya kamata ba sannan kuma ta ƙara da cewar.Ta ce "A matsayi na ƙasa da ƙasa kasashen biyu sun amince da shawarar' da aka bayar amma a matsayi na Turai bakiya ɗaya ba akai ga cimma daidaituwa ba.Merkel Ta kuma ce Burtaniya na da mahimmanci a matsayin mamba a ƙungiyar Tarayyar Turan dangane da kokowar da ake yi ta ci gaban nahiyar.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Zainab Mohammed Abubakar