Salu Jibbo ya gana da ´yan takara zaɓen shugaban ƙasa a Nijar
March 11, 2011Shugaban mulkin sojan Jamhuriya Nijar, Janar Salu Jibbo ya gana da´yan takara zaɓen shugaban ƙasa zagaye na biyu, wato Mahamadu Isufu na jam´iyar PNDS-Tarayya da Seini Umaru na MNSD-Nasara.
An yi wannan ganawa tare da halartar shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta CENI, mai shari´a Abdruhaman Ghusman.
Shugaban ya yi kira ga ´yan takara biyu su gargaɗi magoya bayan su domin shirya wannan zaɓe cikin tsanaki, a nasa gefe ya yi alƙawarin ɗaukar dukan matakan da su ka dace domin shirya wannan zaɓe cikin adalci a ranar 12 ga watan Maris.Ranar juma´a a ka kammalla yaƙin neman zaɓen cikin kwanciyar hankali.
Za ku ji ƙarin bayani a cikin rahotanin guda biyu ɗaya daga Yahouza Sadissou game da ƙarshen yaƙin nema zaɓe, sai kuma na biyu daga wakilinmu Gazali Abdu Tasawa game da ganawa tsakanin shugaban ƙasa da yan takara.
Mawwallafi: Yahouza Sadisou Madobi
Edita: Umaru Aliyu