Sakamakon zaɓen ´yan majlisar dokoki a Nijar
March 16, 2011Talla
Ranar 31 ga watan Janiaru na wananshekara a ka shirya zaɓen yan majalisar dokoki a Jamhuriya Nijar tare da zagayen farko na zaɓen shugaban ƙasa.
Bayan hukumar zaɓe mai zaman kanta wato CENI ta gabatar da sakamakon wucin gadi ga kotu, a wannan Larabar kotin ta yanke hukunci ƙarshe.
Ko mi wannan hukunci ya ƙunsa? sai ku saurari rahoton da wakilinmu daga birnin Yamai Gazali Abdou Tasawa ya aiko.
Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Ahmad Tijani Lawal