Sakamakon zaɓen majalisar dokoki a Chadi
February 28, 2011Bisa rahotannin sakamakon wucin gadin da ke fitowa daga Chadi yanzu, Jam'iyar shugaban ƙasar, Idriss Deby da muƙarraban sa, sun lashe zaɓen majalisar dokokin ƙasar da aka gudanar a ranar 13 ga wannan watan na Fabrairu da gagarumin rinjaye.
Yaya Mahmat Liguita, shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta, ya ce sakamakon na nuna cewa Jamiyyar Patriotic Salvation Movement (MPS) da sauran jam'iyun da ke ƙawance da ita, sun lashe kujeru 133 a cikin kujeru 188, amma suna jiran kotun tsarin mulkin ƙasar ta ba da tabbacin hakan.
Babbar jam'iyar adawa ta National Union for Democracy and Renewal, a ƙarƙashin jagorancin Saleh Kebzabo ta lashe kujeru 11.
Shugaban hukumar zaɓen dai ya ce fiye da kashi 50 na waɗanda suka cancanci yin zaɓe suka fito suka kaɗa ƙuri'un su, kuma jam'iyu guda 16 daga cikin jam'iyun ƙasar fyie da 100 sun sami aƙalla kujera ɗaya a majalisar dokokin.
Mawallafiya: Pinaɗo Abdu
Edita: Mohammad Nasiru Awal