Sakamakon gasar wasannin FIFA Club World Cup 2025
June 15, 2025Talla
A gasar cin kofin zakarun kungiyoyin kwallon kafa ta duniya wato FIFA Club World Cup da aka fara a wannan Lahadi, a wasan farko kungiyar kwallon kafa ta Inter Miami FC ta Amurka ta yi canjaras da takwararta ta Al Ahly FC ta Masar, babu ci a tsakaninsu.
Wasa na gaba da Inter Miami ta Lionel Messi za ta buga ranar Alhamis mai zuwa, za ta kara da FC Porto ta Portugal a birnin Atlanta na Amurka, yayin da ita kuma Al Ahly ta Masar za ta fafata da Palmeiras ta Brazil.
Karin bayani:Saudiyya za ta karbi bakuncin FIFA a 2034
Nan gaba a wannan Lahadi Bayern Munich ta nan Jamus za ta kece raini da Auckland City ta kasar New Zealand.