Rikice-rikiceGabas ta Tsakiya
Gaza: Yaushe za a daina zubar da jini?
August 25, 2025Talla
Shugaba Donald Trump na Amurka ya bayyana cewa, Isra'ila ba ta sanar da shi ba kafin kai wannan harin ba. Sojojin Isra'ilan sun kai hari a asibitin Nasser da ke yankin kudancin Zirin Gaza, harin da ya halaka 'yan jarida biyar da ke aiki da kamfanin dillancin labarai na Reuters da na Associated Press da gidan talabijin na Al Jazeera da kuma wasu kafafen yada labarai.
Hadaddiyar kungiyar 'Yan Jaridu ta Falasdinu ta bayyana cewa, sama da 'yan jarida 240 ne suka halaka tun bayan fara yaki tsakanin Isra'ila da kungiyar Hamas mai gwagwarmaya da makamai a yankin na Zirin Gaza. Koda yake akwai rahoton da ke nuni da cewa 'yan jarida 192 ne suka halaka, tun bayan fara yakin a ranar bakwai ga watan Oktobar 2023.