Yaushe tasirin Rasha a Afirka zai ragu?
June 11, 2025Ranar 31 ga watan Mayun wannan shekara, manyan motoci dauke da makamai na zamani suka ratsa birnin Bamako fadar gwamnatin kasar Mali. Rahotannin sun nunar da cewa makaman sun fito ne daga tashar jiragen ruwan birnin Conakry fadar gwamnatin kasar Guinea, kafin isa kasar Mali wadda take dasawa da Rasha. Hakan na nuna yadda Rasha take taka takunkumin kasashen Yammma, kamar yadda kamfanin dillancin labaran AP ya gano.
Mali ta fada matsalolin tsaro fiye da shekaru 10 da suka gabata, tare da samun juye-juyen mulki sau biyu a shekara ta 2020 da kuma 2021. A shekarun baya dakarun kasar Faransa sun taka muhimmiyar rawa, wajen yaki da kungiyoyin tsageru masu dauke da makamai a kasashen Mali da Burkina Faso da kuma Jamhuriyar Nijar.
Amma daga bisani Faransa ta janye dakarunta, bayan juye-juyen mulkin sojoji da aka samu a kasashen uku. Ita dai Rasha ta zabi tashar jiragen ruwan birnin Conakry fadar gwamnatin kasar Guinea a matsayin hanyar kai wa kasashen yankin Sahel, abin da masanin yankin Seidik Abba shugaban Cibiyar Kula da Harkokin Kasashen yankin na Sahal ya ce ba abun mamaki ba ne kasancewar kasashen biyu na alaka tun tsawon lokaci.
Sai dai Rida Lyammouri masanin harkokin kasashen yankin Sahel da ke Cibiyar Kula da Lamuran Kasashen Kudancin Duniya a kasar Maroko, na ganin akwai sauran aiki kafin kawo karshen matsalar tsaron. Sannu a hankali aikin dakarun Rasha na maye gurbin sojojin haya na kamfanin Wagner da aka karya tasirinsu tun shekara ta 2023, bayan boren da shugaban kamfanin Marigayi Yevgeny Prigozhin ya jagoranta a Rashan. Akwai shaidar yadda Rasha take daukar irin wannan sojojin da take turawa, inda take ba su gata na musamman.