Sabon yanayi na tabarbarewar tsaro a Najeriya
April 23, 2025Sake bullar wadannan hare-hare a wasu jihohin Najeriyar na daga hankali sosai saboda kama hanyar komawa yanayin da aka yi sallama da shi a watanni baya. Kalaman da ake amfani da su na ‘yan bindiga ne ke kara hare-haren da ba'a san ko su wanene ba na sanya tambayoyi a kan su wanene ke kai wannan harin?
Kama daga jihohin Benue da Plato da ma jihar Edo yanzu ga jihar Niger da gwamnati ta kafa dokar hana zirga zirgar Babura a birnin Minna duk a kokarin katse hanzarin bata gari da ‘yan ta'adda da ke shigar burtu. Dr Kabir Danladi Lawabti mai sharhi a kan al'ammuran yau da kullum a Najeriyar na mai bayyana munin halin da ake ciki.
‘'Wannan abin da ke faruwa yana da mugun hatsari a Najeriya domin akwai kasashe da yawa da ba wanda ya zaci zasu shiga halin da suke ciki na yakin basasa, don haka dole ne idan ana so kasa ta zauna lafiya masu aikata wannan laifi a kira su da sunansu, kuma a bar danganta su da wata kabila''
An dai kai ga ambato bullar wata sabuwar kungiyar ‘yan ta'adda ta Mamuda wacce ta zafafa miyagun hare-hare da take kaiwa a yankin arewa maso tsakiyar Najeriyar. Ko da yake gwamnatin Najeriyar ta musanta bullar wannan kungiya amma ga Dr Kabir Adamu masani a fannin tsaro kuma shugaban cibiyar Beacon da ke Abuja ya bayyana man fahimtarsa.
‘'A fahimtarmu wadanda ke kai wadannan hare-hare suke kashe jama'a ‘yan bindiga ne wadanda suka bijere wa doka, a cikinsu akwai 'yan ta'adda da kuma kungiyoyi da ke da alaka da bangaranci haka akwai na cikin gida da kuma na kasa da kasa''
Amma wane mataki gwamnatin ke dauka don dakile matsalar musamman a yanzu da ake nuna cewa maharan na tsallakowa ne daga kasashe makwabta.
Najeriyar dai na kokarin sake farfado da dangantar soja tsakaninta da Jamhuriyar Nijar domin katse hanzarin ‘yan ta'addan da ke bi ta kasashen Mali da Libya da Nijar zuwa Najeriya musamman saboda rushewar gwamnatin kasar Syria.