Sabon tsarin IIimi a Jamhuriyar Nijar
September 26, 2011A jamhuriyar Nijar a daidai lokacin da ya rage mako ɗaya daliban makarantun boko na pramare da sakandare na ƙasar su koma ajujuwa bayan kammala dogon hutu, wasu ƙungiyoyin malaman makarantun boko dama na iyayan yara 'yan makaranta sun soma nuna rashin amincewarsu da wani matakin da gomnatin ta ɗauka na janye tsarin shirya jarrabawar shiga sakandare daga bana. Wannan dai yana daga cikin wani garan bawul da gwamnati ta yi wa tsarin karantarwa a kasar ta Nijar.
Babban taron mahawara kan harakokin ilimi na ƙasa na shekarar da ya wakana a tsakiyar wannan wata na Satumba ne ya yi wannan garanbawul kan harakar ilimi na cire jarabawar shiga sakandare a Nijar wato CFEPD. Daga cikin tsarin karantarwa na kasar ta Nijar wannan kuwa domin baiwa illahirin dalibban da su ka kai a aji na shida damar shiga makarantar sakandare ba tare da fuskantar tarnaƙin jarabawar karshen shekara ba, wacce alkalumman ma'aikatar ilimi ta kasa su ka nuna cewa daga cikin dalibai 346 kai daga cikin ɗalibai dubu daya ke cin jarrabawar a shekara, abunda kuma ke kawo cikas ga burin gwamnatin Nijar na ganin mafi yawancin dalibai sun mallaki a ƙalla ilimi na sakandare kafin su bar karatu.
To sai dai ga bisa dukkan alamu wannan mataki bai gamsar da wasu kungiyoyi da ke da ruwa da tsaki cikin harakokin ilimi ba. Ga misali ƙungiyar malaman makarantun pramare ta SNEB na daga cikin masu adawa da wannan sabon tsarin kamar dai yanda malam Adamu Asmane ɗaya daga cikin shugabannin ƙunguiyar ya yi wa wakilinmu Gazali Abdou Tasawa ƙarin haske.
Kazalika itama dai ƙungiyar iyayan yara yan makaranta ta Nijar a ta bakin shugabanta Alhaji Abdu Mai Tambola ta yi tir da Allah wadai da wannan tsari da gwamnati ta fitar
Hukumomin ƙasar Nijar dai na masu kafa hujjarsu ta ɗaukar wannan mataki da yanda a wasu ƙasashen renon Faransa irinsu Jamhuriyar Benin aka ƙaddamar da irin wannan tsari. To sai dai a cewar Malam Ƙasum Isa tsohon shugaban ƙungiyar malaman makarantun boko ta SNEN kwararre akan sha'anin ilimi hujjar wasu kasashe sun yi aiki da wannan tsari ba hujja ba ce.
Hasali ma Malam Ƙasum Isa ya bayyan cewa ƙasashe da kungiyoyi masu hannu da shuni ne da basu nufin kasashen mu da ci gaba su ke tilastawa gomnatocin ƙasashemmu kaddamar da irin wannan tsari.
Sai dai lokacin da wakilin na mu ya tuntubi babban daraktan kula da tsarin karatun pramare a jamhuriyar Nijar kan wannan batu, ya ce da shi ba zai ce uffan ba kan batu, domin kuwa har yanzu babbu wata takarda da ya samu daga ɓangaran magabatansa da ke tabbatar da cewa gomnati za ta yi amfani da wannan sabon shawarar da taron ilimin na ƙasa ya dauka
A ƙasa: Kuna iya sauraron sautin rahoton wakilanmu Gazali Abdu Tasawa daga Yamai da Babangida Jibril daga Kano kana da hira da Dakta Abubakar Mu'azu na jami'ar Maiduguri.
Mawallafa: Gazali Adu Tasawa/Halima Balaraba Abbas
Edita: Usman Shehu Usman