Trump ya cika kwanaki 100 a karagar mulki
April 29, 2025Gwamnatin Shugaba Donald Trump ta Amurka ta cika kwanaki 100 kan madafun iko, yayin da ake batun rage yawan ofisoshin jakadancin kasar musamman a nahiyar Afirka da ma dangantaka mai rauni tsakanin gwamnatin ta Trump da kasashen nahiyar.
Karkashin wani kudiri, jaridun kasar ta Amurka sun ruwaito cewa Shugaba Donald Trump na shirin rufe ofisoshin jakadancin kasar 27 da ke nahiyar Afirka. Sai dai daga bisani Sakataren harkokin wajen kasar Marco Rubio ya karyata rahotannin. Ana danganta matakin na rufe wasu ofisoshin jakadancin domin tsuke bakin aljihu.
Masana irin su Alex Vines da ke jagoranci harkokin Afirka a cibiyar kasashen ketere Chatham da ke birnin London na Birtaniya na ganin duk da jan kafa wajen nada jakadun na kasashen duniya, nahiyar Afirka tana baya ga dangi.
"Gwamnatin Trump ba ta ba da muhimmanci wajen nada jakadu a kasashen ketere ba. Kawo yanzu gwamnatin jakadu uku ta ba da sunansu domin tantancewa zuwa nahiyar Afirka: Kasashen Afirka ta Kudu da Moroko gami da Tunisiya. Duk sauran kasashen ko suna da jakadu ko kuma ana jiran wadanda za a nada."
Babu dai jakadun a kananan kasashen Afirka da kuma manya masu karfin tattalin arziki na nahiyar kamar Nigeria, Kenya, Masar da Habasha, kuma tun gwamnatin Donald Trump ta farko babu abu mai tasiri da nahiyar ta samu kamar yadda Steven Gruzd na cibiyar Afirka da Rasha da ke Afirka da Kudu ya bayyana.
"Nahiyar Afirka ba rawar da ta taka lokacin mulkin Trump na farko. Ya caccaki nahiyar tare da watsi da ita kuma bai kai ziyara ba. Ban ji mamaki ba galibin kasashen Afirka masu tasiri babu jakadun kasar ta Amirka. Wannan ya nuna irin abin da yake da tasiri a wajen Trump. An nada Leo Brent Bozell III mai matsanancin ra'ayin mazan jiya domin tantancewa a matsayin jakada a Afirka ta Kudu.
Matakin kassarawa da rufe ma'aikatan gwamnatin Amurka da attajiri Elon Musk ke jagoranci yake daukar hankalin gwamnatin. Rage ofisoshin jakadancin, wata manufa ce ta gwamnatin. Christopher Isike daraktan cibiyar harkokin Afirka a jami'ar Pretoria ta Afirka ta Kudu ga abin da yake cewa a kai.
"Gwamnatin Trump ba ta amince da matakin hulda da kasashen Afirka a dunkule ba. Tun lokacin mulkinsa na farko mun gane cewa yana son kulla yarjejeniya da kowace kasa a matsayin ta na kasa."
Zai yi wuya gwamnatin ta Trump ta tsawaita yarjejeniyar kasuwanci da kasashen Afirka bayan ranar 1 ga watan Oktoban shekarar 2025.