Fafutikar sake dawo da mulkin demokaradiyya a Nijar
September 8, 2025A cikin wata sanarwa da ya fitar sabon gungu na gamayyar kungiyoyin ya yi tsokaci kan fannoni da dama ciki har da neman a saki hambararran shugaban kasar Nijar Bazoum Mohamed da sauran wasu mutane da ake tsare da su.
Sannan ya yi kira da a samar da zaman lafiya a kasar ta Nijar tare da jinjina wa sojojin da ke yaki da matsalar tsaro a kasar.
Ita dai wannan gamayya ta kungiyoyi na fararan hula da na kafofin sadarwa kamar yadda cikin sanarwa suka nunar, sun ce sun kirkira wannan kungiya ce ta G25 Nijar domin fafutikar dawo da tsarin demokaradiyya a kasar ta Nijar, inda suka ce tun bayan juyin mulkin da ya wakana kasar ta Nijar da ma ‘yan Nijar na cikin mawuyacin hali.
Ya zuwa yanzu dai baya ga shi mai magana da yawun kungiyar babu wata masaniya kan ko wanene shugaban wannan sabuwar kungiya da ma mambobinta inda inda a wata kafar sadarwa suka ce sun boye sunayansu ne bisa dalillai na tsaro.
Sai dai kuma da yake magana Mohamed El Kabir, shugaban gamayyar kungiyoyin fararan hula na Synergie masu fafutikar kishin kasa a Nijar ya ce duk wani mai kyakyawan nufi don kasar sa yana fitowa ne ya dauki nauyin abin da ya furta.
Kungiyar dai ta yi fatan ganin an samar da dubaru na musamman kan yaki da ayyukan ta'addanci wanda kowane dan kasa zai kama, inda ta ce za ta dukufa wajen kare hakkoki na demukaradiyya da 'yancin dan Adam cikin zaman lafiya da hadin kan 'yan kasa.