SiyasaArewacin Amurka
Sabon harajin shugaban Amurka Trump kan kasashe ya fara aiki
August 7, 2025Talla
Sabon karin harajin da shugaban Amurka Donald Trump ya lafta wa tarin kasashen duniya ya fara aiki a wannan Alhamis, wanda ya karu daga kashi 10 zuwa 50 cikin 100.
Tuni ma jami'an hukumar kula da shige-da-fice da takwarorinsu na yaki da fasakwauri na Amurka, suka fara karbar harajin hajojin da ke shiga kasar, wanda a baya Mr Trump ya dage shi, kafin sake ba da umarnin karbarsa.
Karin bayani:Trump ya lafta wa kasashen duniya sabon haraji
Shugaba Trump ya nanata cewa matakin na sa sai habaka tattalin arzikin kasar, wanda zai samu karin biliyoyin daloli daga kasashen ketare, wadanda ya ce a baya suna yi wa kasarsa kwange.