Sabon harajin Amurka kan Canada da Mexico ya fara aiki
March 4, 2025A ranar Talata ce sabon harajin da Amurka ta kakaba kan kayayyakin kasashen Canada da Mexico ya fara aiki.
Hakan ya biyo bayan shafe dan lokaci ne ba tare da cimma wata matsaya ba tsakanin Amurkar da kuma kasashen.
Shugaba Trump ya sanar da karin kudin fito kan kasashen ne da suka kasance abokan huldar kasuwancin kasarsa bayan zarginsu da rashin magance shigar bakin haure a Amurka da safafar kwayoyi.
Trump ya lafta harajin kaso 25% ga karafa dake shiga Amurka
A yayin da harajin ke fara aiki, Trump ya ce babu ci gaba da aka samu a kokarin magance shigar miyagun kwayoyi kamar su fentanyl a Amurka.
Hannayen jarin kasar sun fuskanci koma baya a ranar Litinin bayan Trump din ya fada wa manema labarai cewa babu wata kofar da ta rage wa makwabtan nasa ta kauce wa harajin.
China ta yi karin harajin kashi 15% kan Amurka
Firaministan Canada Justin Trudeau ya sha alwashin mayar da martani kan Washington ta hanyar kara kashi 25% na haraji da zarar Amurkar ta fara aiwatar da tata karin.
A wani batun mai kama da wannan kuma China ta ce za ta yi karin kaso 15% kan kaji da alkama da masara da kuma auduga da ke shiga daga Amurka.