Sabon firimiyan Nijar ya kama aiki
April 21, 2011A wani mataki na cika dorewar matakin mai da jamhuriyyar Nijar kan turbar dimokraɗiyya a yau aka yi bikin rantsar da sabon firai minista ƙasar Birji Rafini, a gaban 'yan majalisar dokoki, kamar yadda kundin tsarin mulkin ƙasar ya tanada, wato kafin ya fara aiki sai ya yi wannan rantsuwar.
Girgka sabuwar majalisar ministoci
A wani matakin kuwa a jamhuriyyar ta Nijar ya aka miƙa sunayen sabuwar majalisar ministoci. Shugaban ƙasar ta Nijar Alh. Mohamadu Issufu ya gabatar sunayen membobin sabuwar majalisar ministocin kasar, wadda ta kunshi mutane 24. Shugaban ya bayyana jerin sunayen membobin majalisar ne a cikin wani sabon kudurin doka da ya ɗauka.
A ƙasa kuna iya sauraron satin waɗannan rahotanni daga bakin wakilanmu a Yamai Gazali Abdu Tasawa da Mahaman Kanta
Mawallafi: Ahmadu Tijjani Lawal
Edita: Usman Shehu Usman