Sabbin hare-haren sun salwantar da rayuka a Najeriya
May 12, 2025Talla
Akalla mutane 23 ne rahotanni ke tabbatar da mutuwarsu a jihar Benue da ke a Najeriya, a wasu hare-hare hudu daban-daban da aka gani a jihar a karshen mako.
Hare-haren da suka sake tayar da sabuwar fitina a jihar, sun faru ne a ranar Asabar sakamakon rikicin makiyaya da kuma manoma, a cewar kungiyar ba da agaji ta duniya Red Cross.
Kungiyar ta kuma ce mutane da dama sun jikkata a lamarin.
Wasu daga cikin yankunan da hare-haren suka shafa, sun hada da wadanda suka fuskanci makamantansu a sama da wata guda da ya gabata, inda mutane 56 suka salwanta.
Galibi dai irin wadannan hare-hare kan rikide su koma rikicin addini a jihar ta Benue da ke a tsakiyar Najeriyar.