Sabanin Mali da Aljeriya na tasiri kan tsaron Sahel
April 8, 2025Babu shakka, an dade ana zaman doya da manja tsakanin Aljeriya da Mali da ma sauran kasahen kawancen AES da ke yankin Sahel. Hasali ma, dangantaka tsakanin Aljeriya da Mali ta sukurkuce tun bayan da gwamnatin mulkin sojan Mali ta zargi makwabciyarta Alejriya da yunkurin tayar mata da hargitsi a cikin gida, ta hanyar tallafa wa dakarun 'yan tawayen Abzinawan yankin arewaci, wadanda Malin ke dauka a matsayin 'yan ta'adda. Sannan, Mali ta zargi Aljeriya da kakkabo wani jirginta marasa matuki a Tinzawatene.
Karin bayani: Shekara guda da kafa AES a yankin Sahel
Abdoulaye Diop, ministan harkokin wajen Mali, ya ce wannan yunkuri na Aljeriya ya shafi kasahen AES baki daya, inda ya ce: "Hadin gwiwar shugabannin kasashen AES sun dauki matakin lalata jirgin maras matuki na sojojin Mali a matsayin wani mataki da ya shafi daukacin kasashe mambobin kungiyar, kuma hanya ce ta yada ayyukan ta'addanci tare da taimakawa wajen tada zaune tsaye a yankin."
Sai dai gwamnatin Aljeriya ta musunta zargin, tana mai cewar jirgin da ta harbo ya kutsa sararin samaniyarta har na tsawon kilimoita daya da rabi ba tare da izini ba. Kuma wannan ba shi ne karon farko da jirgin kasar Mali maras matuki na leken asiri ke keta sararin samaniyar ba, lamarin da Algers ta ce ya saba wa ka'idodin kasa da kasa. Tuni, Aljeriya ta sanar da matakin rufe sararin samaniyarta ga jiragen saman Mali, bayan da kasahen uku na Mali da Burkina Faso suka janye jakadunsu daga Algeriya. Sannan, ta janye jakadunta a Nijar da Mali tare da dage zuwan sabon jakadinta a Burkina Faso sakamakon wannan guguwa da ta taso.
Karin bayani: Tasirin rikicin siyasa a harkar tsaro yammacin Afirka
Dangantaka tsakanin Mali da Aljeriya ta samo asali ne tun a shekarar ta1960, lokacin da Mali ta samu 'yancin kai, a daidai lokacin da Aljeriya ke fafutukar ganin ta samu 'yancin kanta daga hannun Faransa. A wancan lokacin, Shugaba Modibo Keita na Mali ya bai wa Abdelaziz Bouteflika da ya yi hijira a Gao da ke arewacin Mali damar aika makamai zuwa Aljeriya domin tallafa wa gwagwarmayar FLN.
A halin da ake ciki dai, kasahen Mali da Nijar sun fice daga cikin rundunar hadin gwiwa ta CEMOC da ke aikin tabbatar da tsaro a tsakanin iyakokin kasahen. Sai dai, wani kwarare a kan sha'anin tsaro Aly Tounkara, ya ce janyewar kasahen ba za ta yi wani babban tasiri ba saboda kusan ba ta aiki sossai. Ya ce: "Ga wadanda ke sane da tabarbarewar alakar da ke tsakanin Mali da Aljeriya a yau, da kuma tsakanin Moritaniya da Mali, sun san cewar wannan hadin gwiwa ba shi da wani tasirin tun can dama."
Karin bayani:Matakan saukaka zirga zirga tsakanin kasashe membobin AES
Sai dai, kasahen Nijar da Burkina Faso na cin moriyar hulda da Aljeriya a fannin makamashi da harkokin kasuwanci na kayan abinci da ke shiga Nijar ta Tamaraset, amma ga shi sun tari aradu da ka.