Sabani a kan tura sojoji wajen zanga-zangar Los Ageles
Shugaban Amurka ya tura dakaru da makamai domin kwantar da tarzomar da ake ci gaba da yi a birnin Los Angeles, wannan dai ba shi ne karon farko da ake takun-saka da gwamnatin kan batun tura sojoji wajen zanga-zanga ba.
Tarzomar adawa da korar baki
A birnin Los Angeles na jihar California, ana ci gaba da gwabza fada tsakanin 'yan sanda da masu zanga-zanga bayan tsare-tsaren da Hukumar Kula da Shige da Fice ta yi. Rahotanni sun ce ‘yan sanda sun yi amfani da barkonon tsohuwa da gurneti da harsasan roba, a kokarin tarwatsa taron jama’a. Masu zanga-zangar dai sun mayar da martani, ta hanyar jifan jami'an tsaro da duwatsu.
Zanga-zangar nema wa kowa hakki
Kamen da hukumomin ke yi, wani bangare ne na sababbin dokokin shige da fice na gwamnatin Republican. Masu suka sun ce ya saba wa ka'ida, kuma hari ne a kan mutane 'yan asalin Latin Amurka. Masu zanga-zangar dai, sun yi ta kiran da a saki wadanda ake tsare da su. Shugabar kasar Mexico Claudia Sheinbaum ta kare bakin haure da ke zaune a kan iyaka ta arewaci, tana mai cewa mutane ne na gari!.
Ana kara tsare mutane
Tun lokacin da Donald Trump ya koma ofis a watan Janairu, aka samu karuwar kamen da Hukumar Kula da Shige da Fice ke yi. A yanzu adadin ya haura mutane dubu 100, a cewar wani rahoto na CBS. Yunkurin ya haifar da koma-baya a fadin kasar. An kama masu zanga-zangar nuna adawa da samamen a Los Angeles masu tarin yawa.
Harsashin roba ya ritsa da wata 'yar jaridar Australiya
Yayin da rikicin ya tsananta, lamarin ya ja hankalin duniya. Wata 'yar jaridar 9News ta Australiya Lauren Tomasi ta sami rauni a kafa, sakamakon harbin ta da harsashin roba da 'yan sanda suka yi yayin da take bayar da rahoto kai-tsaye daga birnin Los Angeles. Sai dai Tomasi ta tabbatar da cewa, tana cikin koshin lafiya kuma ba ta samu rauni ba.
Tura sojojin tsaron kasa, ya sa California daukar mataki
Shugaba Trump ya bayar da umarnin tura dakarun soja 2,000, domin tallafa wa jami'an Hukumar Kula da Shige da Fice ta ICE. A cewar fadar White House, a dauki matakin ne domin " magance rashin bin doka." Ana dai sukar sahihancin tura sojojin, gwamnan jihar California Gavin Newsom ya kira matakin "rashin dacewa" kuma ya ce jihar na shirin shigar da kara a gaban kuliya.
Bala'o'i daga indallahi da tashin hankalin al'umma
Ana tura sojoji domin yin aiki a lokacin afkuwar bala'o'i, a wasu lokutan kuma saboda tashin hankalin al'umma. Duk da haka dokar tayar da kayar baya ta bai wa shugaban kasa ikon tura dakarun soji, domin taimaka wa hukumomin jiha da tabbatar da doka a lokacin tawaye ko tashin hankali. Sai dai ana tura irin wadannan jami'ai ne, tare da amincewar hukumomin jihohi da na kananan hukumomi.
Gayyatar sojoji
Tura sojojin da gwamnatin Trump ta yi, ya zama karo na farko cikin shekaru da dama da wani shugaban kasa ya yi yunkurin hada rundunar tsaron kasar ta wannan hanya ba tare da amincewar gwamna ko kuma bukatar hakan ba. DW, ta yi nazarin sanannun lokutan da aka yi amfani da dokar tayar da zaune tsaye.
A 1957: Makarantar Sakandare ta Little Rock
A 1957 Shugaba Dwight D. Eisenhower ya hada dukkan dakarun Arkansas na kasar, inda ya tura su domin raka dalibai bakar fata tara zuwa makarantar sakandare ta Little Rock. An dauki matakin ne, bayan da gwamna Orval Faubus ya yi amfani da jami’an tsaron jihar wajen hana daliban shiga makarantar da ake nuna wariyar launin fata.
1968: Kisan Martin Luther King Jr.
Kisan jagoran kare hakkin dan Adam Martin Luther King Jr. a ranar 4 ga Afrilun 1968, ya haifar da gangami da tarzoma a fiye da biranen Amurka 100. A martanin da ya mayar, Shugaba Lyndon B. Johnson ya yi amfani da dokar tayar da zaune tsaye wajen dawo da zaman lafiya a babban birnin kasar Washinton D.C. Hakan ya bayar da damar tura sojojin tarayya, domin kwantar da tarzoma.
A 1992: Tarzoma a kan Rodney King
A 1992 Shugaba George H. W. Bush ya yi amfani da dokar tayar da kayar baya, kuma ya bayar da umarnin tura daruruwan dakarun tsaron kasa zuwa Los Angeles. Wannan na zuwa ne bayan kwanaki na tashin hankali, sakamakon wanke jami'an 'yan sanda da aka nuna a bidiyo suna dukan wani direban mota bakar fata Rodney King. Rikicin ya yi sanadiyar mutuwar mutane 60, yayin da fiye da 2,300 suka jikkata.
a 2020: Zanga-zanga a kan kisan George Floyd
A watan Yunin 2020 a lokacin wa'adinsa na farko, Trump ya yi la'akari da yin amfani da dokar tayar da zaune tsaye a matsayin martani ga zanga-zangar da aka yi a kasar baki daya biyo bayan kisan da 'yan sanda sukakashe wani bakar fata George Floyd a Minneapolis. A yawancin jihohin da abin ya shafa kamar Minnesota, gwamnoni sun yi amfani da sojojin National Guard wajen kwantar da tarzoma.