Sababbin hare-haren 'yan bindiga a Nijar
June 1, 2013Wasu 'yan bindiga da ba a san ko su wane ba sun kai hari kan babban gidan yari dake Yamai babban birnin Jamhuriyar Nijar, inda suka bude wuta kan masu gadi da misalin karfe uku na yammacin ranar Asabar.
Rahotanni sun bayyana cewa bayan da suka bude wutar, sun yi kokarin kutsa kai cikin gidan yarin, a wani yunkuri da ake zaton na neman kubutar da wasu mutanensu da ake tsare da su a cikin gidan kason birnin na Yamai na tsawon watanni.
Shaidun gani da ido sun tabbatar wa da wakilinmu na Yamai Gazali Abdu Tasawa faruwar wannan lamari.
Hukumomin kasar ta bakin kakain gwamnati kuma Ministan Sharia'a na kasar Moru Amadou, sun tabbatar da mutuwar sojoji biyu yayin da wasu uku suka jikkata, haka nan kuma jami'an tsaro sun yi wa unguwar Maison Economique inda gidan kason ya ke kawanya, tare da takaita zirga-zirgar jama'a da kuma gudanar da sintiri.
Wanann hari dai ya zo ne kwanaki tara bayan da kungiyar MUJAO ta kai wasu tagwayen hare-haren kunar bakin wake a garin Agadez da na Arlit a bisa zargin Nijar din da taka rawa cikin yakin kasar Mali.
Mawallafi: Gazali Abdu Tasawa
Edita: Lateefa Mustapha Ja'afar / MNA