Sa'adi Gaddafi zai ci gaba da samun mafaka a Nijar
September 29, 2011Nijar ta ce bata da niyyar mika dan Gaddafi Sa'adi Gaddafi zuwa ga hukumomi a Libiya domin ya fuskanci shari'a, a cewar Frime Ministan kasar Birji Rafini lokacin wata ziyarar da ya kai Faransa ranar alhamis. Daga farko dai hukumar 'yan sanda ta kasa da kasa wato Interpol ta ce ta sanya sunan Sa'adi mai shekaru 38 da haihuwa, a cikin jerin sunayen wadanda aka fi bida a duniya, kuma ta gargadi kasashen da ke makobtaka da Libiya a ciki har da Nijar, da su mika shi ga hukumomi bisa zarginsa da sama da fadi da kudaden gwamnati lokacin da ya shugabancin hukumar kwallon kafar Libiya. Frime Minista Rafini ya fadawa kamfanin dillancin labarun Faransa AFP a garin Saint Brieuc cewa Sa'adi yana hanun jami'an gwamnati a Nijar kuma ya ce zasu mika shi hanun hukumomin ne kadai idan sun sami tabbacin cewa za'a kamanta aldalci a shariar da hukumomin zasu yi masa
Mawallafiya: Pinado Abdu
Edita : Usman Shehu Usman